17 Disamba 2021 - 20:01
​Najeriya: Gwamnati Ta Ce Babu Wanda Ya San Ranar Kawo Karshen ‘Yan Bindiga A Kasar

Ministan yada labarai na Najeriya Lai Mohammed ya ce babu wani shugaba da zai ce ayyukan ta’addanci za su gushe a shekara mai zuwa.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Gidan rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, Ministan na najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa wata ta manema labarai, kan cewa ko kalubalen tsaron da ake fuskanta a halin yanzu zai kare kafin shugaba Muhammadu Buhari ya sauka a kan karagar mulki a shekarar 2023.

Lai ya ce ba ya tsammani ko shugaba Buhari zai iya cewa za a dakile ayyukan ‘yan bindiga a shekara mai zuwa, yana mai cewa tamkar a ce za a kawar da barayi ne a shekara mai zuwa.

Ministan ya ce, cewa Buhari ba shi da sauran wani abin da zai tabuka a kasar ba gaskiya ba ne, yana mai danganta haka da cewa batu ne kawai na siyasa.

Wannan furuci an ministan yada labaran na gwamnatin Najeriya, yana a matsayin martani ne ga wani furuci da tsohon shugaba Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi ne a gaban wani taro, inda ya bayyana cewa Buhari ya yi abin da zai iya yi, kuma yanzu babu wani abin da kuma zai iya yi da sunan gyara gyara Najeriya.

342/